WASHINGTON, DC - Da yake jawabi a taron shekara na Majalisar Dinkin Duniya da ake kira UNGA a takaice, shugaba Buhari ya bayyana cewa kasashen duniya na fuskantar sabbin matsaloli, mafi girma a cikinsu sune tashe-tashen hankula, yaduwar makamai, ta'addanci, tsattsauran ra'ayi, amfani da fasaha ta hanyar da bata dace ba, sauyin yanayi, kwararar bakin haure, da bambance-bambance wajen samun damar inganta rayuwa.
Duk da kalubalen da kasashen ke fuskanta, Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewa za ta yi tsayin daka idan mambobinta suka hada kai don daukar matakin da zai amfani kowa.
Daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta a baya-bayan nan shine rikicin Ukraine wanda ya janyo matsalolin da kusan ba a taba ganin irinsu ba a wannan zamanin.
Irin wannan rikici zai janyo mummunan sakamako a gare mu duka, wanda zai kawo cikas a damarmu ta yin aiki tare don magance rikice-rikice a wasu wuraren, musamman a Afirka, Gabas ta Tsakiya da Asiya.
Buhari ya kara cewa, wannan shine karon farko da suka yi taron a birnin New York ba tare da matakan kariyar annobar COVID-19 ba, kamar yadda aka gani cikin shekaru uku da suka wuce. Annobar ta ratsa kan iyakoki kamar wutar daji, inda ta janyo bakin ciki da mace-mace.
Abin farin ciki shine, mun kuma shaidi gagarumin ci gaba ta fannin kirkire kirkire daga kwararrun da suka samar da rigakafin cutar. An cimma wadannan nasarorin ne da taimakon abokan hulda da hadin gwiwar kasa da kasa.
Ya kuma ce, ina farin cikin fada muku cewa a Najeriya, hukumomin lafiyar kasar sun yi iya kokarinsu sun kuma kulla hadin gwiwa da kasashe abokan huldarsu, tare da shirin COVAX wanda ya kunshi kasashe da dama da kuma kungiyoyi masu zaman kansu kamar Gidauniyar Bill da Melinda Gates.