Yau Jumma’a ce ake sa ran Majalisar Dinkin Duniya zata saki wani rahoto da zai nuna dalla dalla zargin laifukan yaki da cin zarafin bil’adama, da aka aikata a jamhuriyar demokuradiyyar kwango.
Ofishin kula hakkin bil’adam ana MDD yace rahoton zai nuna lamari daban daban fiye da dari shida, daga 1993 zuwa 2003, inda aka kashe ko aka jikkata, ko cin zarafin dubun dubatan mutane.
Galibin wadanda wan nan al’amari ya rutsa da su mata ne da yara.Wan nan danyen aikin ya auku ne a lokacin yakin basasar kasar na tsawon shekaru goma,da ya janyo sojoji daga kasashe makwabta suka shiga ciki.
Kasashen Rwanda,Uganda,da Angola tuni sun ki amincewa da rahotanni dake zargin sojojinsu da aikata laifukan yaki a Kwango.