Babban baturen ‘Yansandan kasa da kasa, ko Interpol, yace nan bada jumawa ba,za’a fuskanci karin barazanar ta’addanci daga mayakan sakai dake da’awar Islama a Somalia,fiyeda da ta takwarorinsu dake Afghanistan.
Ronald Noble ya gayawa kamfanin dillancin labaran Asscoiated Press jiya Alhamis cewa, jami’an tsaro suna ganin Karin take taken ta’addanci dake samo asali a Somaliya.Yace Kungiyar Interpol ta hakikance nan da shekaru biyar zuwa 10 Somaliya zata zarce Afghanistan a barzanar ta’addanci.
Shekaru masu yawan gaske rabon Somaliya da gwamnati sahihiya, kuma galibin kasar tana hanun mayakan sakai dake da’awar islama.
Ahalin yanzu kuma, jami’an Amurka sunce an gabatar da tuhuma kan wani dan shekaru 26 dake da zama a abirnin Chicago, kan zargin yana shirin balaguro zuwa Somaliya, domin shiga kungiyar al-shabab mai alaka da al-Qaida.