Ukraine Ta Soma Kera Manyan Makaman Yaki

  • Murtala Sanyinna
A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na X, Zelenskyy ya ce makamin na jirgin sama maras matuki mai suna "Peklo" - wanda ke nufin "wuta" a harshen kasar Ukraine - yana cin nisan zangon kilomita 700, da karfin gudun kilomita 700 a cikin sa'a guda.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya gabatar da sabbin jiragen yaki maras matuki samfurin "Peklo" da ake kerawa a wata masana'anta ta kasar Ukraine, wanda a cewarsa tuni aka kai kashin farko na jiragen da aka kera ga sojojin kasar.

A wani hoton bidiyo da ofishinsa ya fitar, ana iya ganin Zelenskyy yana rangadin masana'antar a wani wuri da ba’a bayyana ba, tare da babban kwamandan sojin Ukraine Oleksandr Syrskyi da wasu jami'ai.

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na X, Zelenskyy ya ce makamin na jirgin sama maras matuki mai suna "Peklo" - wanda ke nufin "wuta" a harshen kasar Ukraine - yana cin nisan zangon kilomita 700, da karfin gudun kilomita 700 a cikin sa'a guda. Ya ce tuni da makamin ya tabbatar da ingancinsa na yaki.

Jami'an Ukraine sun ce jiragen suna da tsada kuma ana kwatanta su da wasu makamai masu linzami da Rasha ta kera ta fuskar aikinsu.

Zelenskyy ya fada a cikin bidiyon cewa, "yana da mahimmanci yadda masu kare mu suka karbi irin wadannan makaman na zamani na Ukraine," ya ci gaba da cewa "yanzu aikin da ke gaba shi ne ci gaba da habaka samar da kayan aiki da kuma amfani da su."