Ukraine Ta Bukaci FIFA Ta Hana Iran Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya A Qatar

Magoya bayan kungiyar 'yan wasan Ukraine

Wannan kira na zuwa ne makonni uku gabanin Iran ta kara a wasanta na farko da Ingila a rukunin B.

Hukumar kwallon kafar kasar Ukraine, ta yi kira ga hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, da ta cire Iran a cikin jerin kasashen da za su halarci gasar cin kofin duniya, saboda tana take hakkin bil adama tare da aika makamai ga dakarun Rasha.

A ranar 21 ga watan Nuwamban nan za a fara gasar, wacce kasar Qatar za ta karbi bakunci.

Wannan kira na zuwa ne makonni uku gabanin Iran ta kara a wasanta na farko da Ingila a rukunin B.

Rukunin har ila yau ya hada da Amurka da Wales.

Hukumar ta FIFA, ba ta ce uffan ga wannan bukata ta Ukraine ba, sannan ba ta da hurumin dakatar da wata kasa saboda wani mataki da ya shafi na soji da wata kasa ta dauka.

Rasha da Iran sun musanta zargin da Ukraine ke yi cewa Moscow tana kai hare-haren bama-bamai a Ukraine da jirage mara matuka da Iran ta kera, wadanda ake kira “Shahed.”