Kasar Rasha za ta garzaya kotun da ke sauraren kararrakin tabbatar da da’a a fagen wasanni a ranar Juma’ar nan, don kalubalantar matakin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dauka, na haramta mata buga wasannin shiga gasar cin kofin duniya.
Hukumar kwallon kafar kasar ta Rasha ta ce ta shirya tsaf don shigar da karar a ranar Juma’ar nan tana mai cewa ba a yi mata adalci ba.
Nan da kwana 20 ‘yan wasan Rashar za su kara da Poland a wasannin shiga gasar wacce Qatar za ta karbi bakunci a bana.
Ita dai FIFA ta dauki matakin haramtawa Rasha buga wasannin ne saboda mamaya da ta kai wa Ukraine.
Tun gabanin wannan mataki na FIFA, kasar ta Poland da za ta kara da Rashar, ta janye daga wasan, a wani mataki na yin Allah wadai da kaddamar da yakin da Rashar ta yi akan Ukraine.
Baya ga fagen kwallon kafa, akwai wasu wasanni da ake yi a sassan duniya da aka haramtawa Rasha shiga gasarsu saboda wannan mamaya da ta yi wa Ukraine.