Ukraine, Amurka Sun Kulla Yarjejeniya Kan Ma’adinai – Jami’in Ukraine

Shugaban Amurka Donald Trump tare da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy

Ukraine da Amurka sun cimma matsaya kan tsarin kulla yarjejeniyar tattalin arziki mai fadi da za ta hada da samun damar mallakar ma’adanan karkashin kasa da babu su a duniya, in ji wasu manyan jami’ain Ukraine uku a ranar Talata.

Jami’an, wadanda ke da masaniya kan lamarin, sun yi magana bisa sharadin a sakaya sunayensu saboda ba’a ba su izinin magana a bainar jama’a.

Daya daga cikinsu ya ce Kyiv na fatan sanya hannun kan yarjejeniyar don tabbatar da ci gaba da bayar da tallafin sojin Amurka da Ukraine ke bukata cikin gaggawa.

Da yake magana da manema labarai a ofishin shugaban kasa, Donald Trump, ya ce ya ji cewa Zelenskyy na zuwa, ya kuma kara da cewa “babu komai a wurina, idan ya so, kuma yana iya sanya hannun tare da ni.”

Za’a iya sanya hannun kan yarjejeniyar nan da ranar Juma’a mai zuwa kuma an shirya tsaf game da tafiyar shugaban Ukraine Volodymyr zuwa Washington don ganawa da Trump, a cewar daya daga cikin jami’in Ukraine.

Wani jami’in ya ce yarjejejeniyar za ta ba da dama ga Zelenskyy da Trump su tattauna batun ci gaba da bayar da tallafin soji ga Ukraine, dalilin da ya sa Kyiv ke son kammala yarjejeniyar.

Trump ya kwatanta wannan matsaya da aka cimma a matsayin “babbar yarjejeniyar,” wacce za ta kai ta tiriliyan na daloli.