Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firai Ministan Burtaniya Ya Gana Da Trump Kan Ukraine


USA-BRITAIN/
USA-BRITAIN/

Starmer zai yi kokarin jarraba kasadar diflomasiya ta hanyar ba da kariya ga mahukuntan birnin Kyiv ba tare da ya fusata Trump ba, wanda tattaunawarsa da gwamnatin Shugaba Vladimir Putin na Rasha ta baiwa Turai matukar mamaki.

Shugaban Burtaniya Keir Starmer ya gana da Shugaban Amurka Donald Trump a fadar White House a yau Alhamis domin yunkurin gamsar da takwaransa ya dauki alkawarin ba da kariya ga kasar Ukraine a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita wuta da Rasha.

Firai Ministan Burtaniya ya nemi ya dora a kan ziyarar da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron ya kai birnin Washington a ranar Litinin.

Sai dai shugaban na Faransa yace tattaunawarsa da Trump a kan cikar shekaru 3 da mamayar Rasha a Ukraine ta nuna cewa akwai mafita duk da fargabar da ake da ita ta samun baraka tsakanin kasashen.

A nasa bangaren Starmer ya yi kokarin jarraba kasadar diflomasiya ta hanyar ba da kariya ga mahukuntan birnin Kyiv ba tare da ya fusata Trump ba, wanda tattaunawarsa da gwamnatin Shugaba Vladimir Putin na Rasha ta baiwa Turai matukar mamaki.

Manya a cikin muradan Starmer su ne samun tabbaci daga Trump na cewa Amurka za ta samar da da kariya daga hare-hare ta sama da musayar bayanan sirri da safarar kayayyakin bukatun soja domin tallafa wa dakarun Turai din da za’a tura Ukraine domin sa idanu a kan tsagaita wuta.

Mahukuntan biranen London da Paris ne ke jagorantar shirin tura “rundunar kawar da fargaba” ta akalla sojoji 30, 000 domin ba da kariya ga Ukraine bayan karewar yaki.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG