UEFA: Bellingham Zai Dawo Buga Wasa Bayan Jinya

Bellingham, hagu da Mbappe, dama

Bellingham ya sha fama da raunin kafa kuma bai buga wasa ba tun farkon wasan La Liga na Madrid da aka yi da Mallorca a watan Agusta.

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce 'yan wasan tsakiya Jude Bellingham da Aurélien Tchouaméni za su kasance a shirye don wasan farko na Real Madrid a gasar zakarun Turai, bayan rashin buga wasan La Liga a karshen makon nan.

Ancelotti ya ce mai tsaron baya Éder Militão shi ma zai kasance cikin koshin lafiya don fuskantar Stuttgart a ranar Talata a filin wasa na Santiago Bernabeu. Militão bai yi atisaye a ranar Litinin ba.

Bellingham ya sha fama da raunin kafa kuma bai buga wasa ba tun farkon wasan La Liga na Madrid da aka yi da Mallorca a watan Agusta.

Wannan zai kasance wasan farko na gasar zakarun Turai ga tawagar tun bayan da suka sanya hannu kan tauraron Faransa, Kylian Mbappé, wanda ake sa ran zai fara buga wasa a ranar Talata.