Kamfanin wutar lantarki na birnin Tokyo yace an fitar da ma’aikata daga ginin wata tukunyar ma’aikatar yau lahadi, bayanda aka sami tururin nukiliya fiye da kima. Kakakin kamfanin TEPCO ya shaidawa manema labarai cewa minzamin tururin nukiliyan da aka samu a ruwan da ya taru a tukunyar nukiliya ta biyu, ya ninka har sau miliyan goma abinda ya kamata ya kasance, daga ninki dubu daya da dari biyu da aka samu jiya asabar. Hukumar kula da ayyukan makamashin nukiliya da kare lafiyar masana’antu ta kasar japan tace minzanin gwajin karfin tururi nukiliya na nuni da cewa, yawan tururin a ruwan teku dake kusa da masana’antar nukiliya ta Fukushima ya haura yadda ya kamata har sau dubu da dari biyu. Jami’an sun ce sun gano sinadarin Iodine a cikin tekun Paficic kimanin tazarar mita dari uku da manana’antar. Hukumar kula da ayyukan makamashi da lafiyar masana’antu tace rabin litar ruwa ya kunshi yawan tururi nukiliya da mutum zai iya fuskanta a shekara. Sai dai jami’an suka ce nan da nan tekun zai dama ruwan da yake dauke da gubar kuma, bashi da wani hadari ga halittu dake cikin ruwa ko kuma illa ga abincin da ake samu daga cikin teku.
Gurbacewar ruwan tekun, shine alama ta baya bayan nan da take nuni da cewa, tururi mai guban yana yaduwa. An kuma sami tururin nukiliya wannan makon a birnin Tokyo da kuma yankunan dake kusa. Yayinda aka kuma sami tururin nukiliya a kayan lambu da kuma madara daga gonakin dake kusa da Fukushima, abinda ya sa kasashe da dama hana shigo da abinci daga yankin. Ana kuma ci gaba da kokarin kwashe gurbataccen ruwan dake cikin ginin masana’antar, bayanda aka kwantar da ma’aikata biyu sakamakon kuna da suka yi da tururin nukiliyan lokacin da suka tsoma kafa a gurbataccen ruwan. Jami’an dake aiki a masana’antar sunce basu san ko daga ina gurbataccen ruwan yake bullowa ba.