Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Japan Ta Daga Matakin Yiwuwar Hadarin Nukiliya Zuwa kwaloluwa


Tashar nukiliyar Fukushima da ta lalace kenan ke hayaki.
Tashar nukiliyar Fukushima da ta lalace kenan ke hayaki.

Hukumar Kiyaye Hadura a Tasoshin Nukiliyar Japan ta daga matakin kasadar yiwuwar hadari a tashar nukiliyar da ta lalace daga 5 zuwa 7, wanda wannan shi ne mafi tsanani a ma’aunin kasa da kasa.

Hukumar Kiyaye Hadura a Tasoshin Nukiliyar Japan ta daga matakin kasadar yiwuwar hadari a tashar nukiliyar da ta lalace daga 5 zuwa 7, wanda wannan shi ne mafi tsanani a ma’aunin kasa da kasa.

Kafafen yada labaran Japan sun fadi yau Talata cewa Hukumar kiyaye Hadura a Tasoshin Nukiliya da Kamfanoni ta yanke wannan shawarar ce bayan da ta gano cewa tururin gubar da ke sacewa daga tashar nukiliyar Fukushima Daiichi na tsawon awoyi bayan girgizar kasar ran 11 ga watan Maris da kuma ambaliyar ruwan tsunami ya kure mataki mafi muni. Su ka ce tuntuni sacewar tururi mai gubar ta lafa.

Amman sai ga shi kuma wata wuta ta tashi a wannan lalatattar tashar nukiliya a yau Talata, to amman rahotanni sun nuna cewa tuni aka kashe.

Gwamnatin ta kuma fadada yankunan da za a kwashe mutanensu da ke zaune zagaye da tashar nukiliyar Fukushima saboda yawan tururi mai gubar da ke ta bazuwa a wurin tun bayan ambaliyar tsunami na watan jiya.

Wani mummunan hucin girgizar kasar da ta wajajjaga arewa maso kudancin Japan ran Litini ya hallaka mutane biyu ya kuma katse wutar lantarki na tsawon ‘yan lokuta a tashar nukiliyar ta Fukushima.

Hucin girgizar kasar ta ranar Litini ta auku ne ‘yan awoyi bayan da ‘yan Japan su ka kammala addu’o’in tunawa da girgizar kasar da ta auku wata guda day a gabata ya ji ma wuraren da ke gabar arewa maso gabashin kasar, ya hallaka dubbai ya kuma kawo wannan matsala ta nukiliya.

XS
SM
MD
LG