Rikicin kan iyaka tsakanin Isra'ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon na kara ta'azzara a 'yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar yakin Isra'ila da Hizbullah. Harin da aka kai a kan iyakar arewacin Isra'ila ya kai ga kwashe dubban mutane daga yankunan biyu.
A jawabin da Erdogan ya yi wa 'yan majalisar dokoki na jam'iyyarsa ta AKP a majalisar dokokin kasar ya ce Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu na shirin gudanar da yakin Gaza zuwa yankin.
"Da alama a yanzu Isra'ila ta mayar da idanunta kan Lebanon bayan da ta lalata da kuma kona Gaza, muna ganin kasashen yammacin duniya suna baiwa Isra'ila goyon baya a sakaye," in ji Erdogan.
Ya ce shirin Netanyahu na kawo yakin Gaza zuwa yankin zai haifar da wani babban bala'i, yana mai cewa goyon bayan da kasashen yamma ke baiwa Isra'ila abin takaici ne.
-Reuters