Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Erdogan Ya Ziyarci Masar Karo Na Farko Tun 2012


Shugaban kasar Türkiye Recep Tayyip Erdogan da shugaban kasar Egypt Abdel Fattah al-Sisi
Shugaban kasar Türkiye Recep Tayyip Erdogan da shugaban kasar Egypt Abdel Fattah al-Sisi

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Laraba ya kai ziyararsa ta farko a Masar tun shekara ta 2012, inda ya gana da Shugaba Abdel Fattah al-Sisi

WASHINGTON, D. C. - Wanda hakan wani babban mataki ne da shugaban na Türkiye ya dauka na sake gina alaka tsakanin kasashen yankin.

Egypt/Turkey
Egypt/Turkey

Erdogan ya ce tattaunawar ta su za ta mayar da hankali ne kan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa zirin Gaza.

Egypt/Turkey
Egypt/Turkey

Shugabannin da dangantakarsu ta yi tsami tun juyin mulkin da sojoji suka yi a Masar a shekara ta 2013 da kuma watsewar kungiyar 'yan uwa musulmi wato Muslim Brotherhood, za su gudanar da wani taron manema labarai bayan sun gama tattaunawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG