Zaben na jiya Lahadi ya sake maida kasar ta Turkiyya kasa mai jam'iyyar siyasa guda, bayan watanni biyar kawai da jam'iyyar ta AKP ta rasa rinjayenta a majalisar dokokin kasar a karo na farko cikin sama da shekaru 10.
Jam'iyyar ta samu kashi 50% ne kawai wato kujeru 316 a Majalisar dokokin mai jimillar kujeru 550.
Babbar jam'iyyar adawa kuma CHP, ta sami dan sama da kashi kashi 25%, wanda ya tabbatar da wagegen gibin nasara ga jam'iyyar AKP fiye da yadda aka zata a baya.
Firaminista Ahmed Davutoglu ya bayyana aniyar hada kan kasa yayin da ya ke jawabi ga magoya baya a birnin Ankara da daren jiya Lahadi.
Ya kuma ce a samar da abin da ya kira sabuwar Turkiyya mai tsarin siyasar da ta dace.
Davutoglu ya sabunta kiraye-kirayen kwaskware kundin tsarin mulkin kasar, wani abu da jam'iyyar AKP ta nema don bai wa Erdogon karin ikon zartaswa.
Amma, duk kuwa da sabon rinjayenta a Majalisar dokoki, har yanzu jam'iyyar za ta kasa samun isassun kuri'u na yin gaban kai, wajen sabunta kundin tsarin mulki.