Tunisiya Da Libya Sun Rufe Iyakokinsu Sakamakon Tashin Hankali

LIBYA-TUNISIA

Tunisiya da Libya sun rufe wata babbar mashigar da ke Ras Jdir saboda fadan da ake yi da makamai a kan iyakar.

WASHINGTON, D. C. - Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Libya ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Talata cewa, "wadansu batagari" sun kai hari kan iyakar kasar. Yankin yana da ɗimbin 'yan Libiya da ke zuwa Tunisiya don kiwon lafiya, da kuma manyan motoci da kayayyaki masu zuwa ta wata hanya.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, sanarwar ta ce "ba za a amince da wannan mataki da haramtattun kungiyoyin suka yi ba, kuma za a dauki matakan shari'a da kuma hukunci mafi tsanani kan wadanda ke da hannu a ciki."

Ma'aikatar ta ce a ranar Lahadin da ta gabata ta girke jami'an tsaro a kan iyakar kasar domin yaki da fasa-kwauri da rashin tsaro.

Gidan rediyon Tataouine na kasar Tunisiya ya fada da yammacin jiya Litinin cewa, Tunisiya ta rufe mashigar domin kare lafiyar 'yan kasar da ke zuwa Libya.