SOKOTO, NIGERIA - Wasu mazauna yankunan iyakokin kasashen biyu sun ta'allaka matsalar kan rashin bude iyakoki daga bangaren Jamhuriyar Nijar, tare da nuna fatar zasu bude don amfanin kasashen biyu.
Cinikayya da sauran huldayya tsakanin al'ummomin Najeriya da Jamhuriyar Nijar sun shiga wani mummunan yanayi tun lokacin da aka rufe iyakokin kasashen biyu, inda jama'a ke fatar samun sauki da zaran an bude iyakokin.
Bayan da kungiyar ECOWAS ta cire takunkumin da ta sakawa Jamhuriyar Nijar gwamnatin Najeriya a makon jiya ta bayar da umurnin bude iyakokin ta da Jamhuriyar Nijar, sai dai kawo yanzu abinda jama'a suka yi fata, musamman mazauna yankunan bai samu ba, kamar yadda wasu mazauna iyakar kasashen ta garin Kamba dake jihar Kebbi ke cewa.
A bangare daya kuma, mazauna iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar a garin Illela ta jihar Sakkwato sun soma ganin sauyi duk da yake Nijar ta ki bude iyakar ta da Najeriya.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa akwai illoli tattare da rashin bude iyakokin daga bangaren Nijar, kamar yadda Dokta Kabiru Alhaji Jabo ke cewa.
Mazauna iyakokin dai duk da yake ba a san dalilin kin bude iyakar ba daga haujin Jmahuriyar Nijar sun nuna fatar bude iyakokin ko da harkokin kasuwanci zasu gudana yadda ya kamata.
Halin yanzu dai dukanin mutanen kasashen biyu na ci gaba da fuskantar matsalolin da rufe iyakokin suka haifar ga rayukan su.
A saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna