Jami’an kasar Tunisiya sunce a kalla mutane 27 aka kashe a wani harin ta’addanci da aka kai kan wata Otal dake kusa da gabar tekun meditareniya.
WASHINGTON, DC —
Jami’an ma’aikatar harkokin cikin gida sunce ‘yan bindigar sun bude wuta ne a kan Otal din Marhaba dake kusa da gabar teku a birnin Sousse wanda fitaccen waje ne da masu ziyara daga nahiyar Turai da arewacin Afirka ke yawan zuwa shakatawa.
Rahotanni na cewa ma’aikatan tsaro sun isa gurin da abin ya faru, kuma akalla ‘dan bindiga ‘daya na daga cikin mutanen da suka mutu.
Tunisiya dai ta jima cikin halin ‘dar ‘dar tun watan Maris, lokacin da wani wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wani gidan tarihi dake birnin Tunis, har suka hallaka wasu ‘yan yawon shakatawa ‘yan kasashen waje, a cikin farmaki mafi muni da kasar Tunisiya ta gani a shekaru masu yawa.