Shugaban kasar Tunisia Zine El Abidine Ben Ali wanda ya kwashe shekaru 23 yana mulkin kasar ya gudu daga kasar,a lokacinda Tunisia take fuskantar mummunar tarzoma da aka juma ba’a irinta ba a kasar.PM Mohammed Ghannouchi yace shine shugaban kasar na wucin gadi.
A yammacin jiya jumma’a ce Bin Ali ya bar kasar da jirgi. Daga bisani a yammacin jiyan,kafofin yada labaran Saudiyya suka bada labrin jirgin Bin Alin ya sauka a birnin Jiddah.
Faransa wacce ta yi wa Tunisia reno tace shugaba Bin Ali bai gabatar mata da bukatar neman mafakar siyasa ba. Ma’aikatar harkokin wajen faransa tace zata tuntubi sabuwar gwamnatin Tunisia kamin ta’a yi la’akari da bukatar.
Kamin ya bar kasar Mr.Bin Ali ya rushe gwamnatinsa ya kuma kafa dokar ta baci. An hana duk wani taro a bainar jama’a,an kuma bai wa jami’an tsaro su harbi duk masu zanga zanga. Jim kadan bayan nan sojojin kasar suka rufe kan iyakoki da sararin samaniyar kasar.
An kashe mutane da dama da har yanzu babu hakikanin adadinsu,sakamkon zanga zanga kan karancin aikin yi da kuma tsadar kayan abinci.