Tunasar da Matasa Mahimmancin Girmama Iyaye

Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon

Majalisar Dinkin Duniya, ta ware kowace daya ga watar Yuli, a matsayin ranar iyaye ta duniya, domin irin rawar da iyaye ke takawa wajen renon 'yayansu.

A hira da wakilimu Ibrahim Garba, yayi da wani matashi Yusuf El-Yakoub Rigasa, yace wannan rana tana da muhimmancin gaske saboda zata rika tunasarwa matasa da saura wadanda basu mutunta iyayensu don su gyara halinsu.

Kan rashin tarbiya tsakanin matasa kuwa, daya daga cikin dalilan da suka janyo haka inji Mallam Rigasa, shine wasu iyayen sun jingine nauyi da ya rataya akansu na yiwa 'yayansu tarbiya, saboda wasu dalilai na yau da kullum.

Daga nan ya shawarwaci matasa wadanda suke son su gama da duniya lafiya su mutunta iyaye.