Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dogaro Da Kai YaFii Dogaro Da Gwamnati


Masu yiwa kasa hidima kimanin 2,300 ne aka yaye a jihar Lagos bayan sun shafe kwanaki 21 suna samun horon sanin kasa da dabi'un al’ummar jihar. Sai dai kuma matsalar samun aikin yi a tsakanin matasan ta zama ruwan dare, inda wasu ke koyon sana'ar hannu domin samun abin dogaro da kai ko da aikin gwamnati bai samu ba.

A shekarun baya dai irin wannan aiki na zama matakin farko na samun aiki ga irin wadannan matasan da suka kammala manyan makarantu a Najeriya. Sai dai tun da Najeriya ta fara fuskantar matsalar tattalin arziki da rashin aikin yi masu yi wa kasar hidima ke fuskantar wahala wajen samun aiki duk da cewa matasan su ne kashi 60 cikin kashi dari din ‘yan Najeriya.

Tuni dai wasu daga cikin masu yi wa kasar hidima su ka fara samar wa kansu mafita, su na koyon sana’o’in hannu domin dogaro da kai.

Malama Rukayyatu Abdulganiyu na daya daga cikin matasan wadda ta shaida wa wakilin muryar Amurka Babangida Jibrin cewa tana koyon dinki domin bata ga kamun ludayyin gwamnati ba.

Saboda matsalar rashin aiki da kuma rashin iya sana’o’in hannu ya sa shugaban Najeriya mai jiran gado Janar Mohammadu Buhari, a lokacin da yake yakin neman zabensa yace za a kara shekara guda ga masu yi wa kasar hidima don koya masu sana’o’in hannu yadda zasu kasance masu dogaro ga kansu. Tuni dai irin wadannan matasan suka rungumi irin wannan damar ta koyaon sana’o’I, wasu matasan da ba su kammala karatu ba su ma sun fara rungumar sana’o’in hannu tun daga matakin sakandare.

Malam Ibrahim Shehu, dalibi ne a Kwalejin kimiya dake unguwar Yaba, jihar Ikko yayi kira ga sauran ‘yan uwansa dalibai dake zaune a gida akan su tashi tsaye don yin wani abu don samun rufin asiri ba sai sun dogara ga gwamnati ba.

Yanzu dai abin jira a gani shine ko gwamnati mai jiran gado zata cika alkawulan da ta dauka na samar wa dumbin matasan Najeriya aikin yi ko kuma a koya masu sana’o’in hannu, abinda kuma zai taimaka wajen zaman kashe wando da na zane da matasan ke yi, lamarin da ka iya sa su shiga wasu harkokin dake barazana ga harkokin tsaro.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG