Dan majalisar dattijai daga jihar Ogun Buruji Kashamu, da hukumar [NDLEA] mai yaki da safara da kuma shan muggan kwayoyi sun sa kafar wando daya inda hukumar ta gurfanar da shi a gaban kuliya.
Koda yake alkalin kotun Ibrahim Buba yace hukumar tayi riga malam masallaci da ta yiwa gidan dan majalisar kawanya kafin samun izinin kotu.
A wata hira da wakilin muryar Amurka, Babangida Jibril, shugaban hukumar Ahmed Giade ya bayyana cewa, sun killace gidan ne, saboda akwai bukatar da gwamatin Amurka ta gabatar ga gwamatin Najeriya tana bukatar a mika shi ga gwamnatin Amurka, bisa tuhumarshi da Amurka ke yi da safarar hodar ibilis, da ya yi zuwa Amurka.
Shugaban hukumar NDLEA ya bayyana cewa, basu sami kama Mr. Kashamu ba saboda ya kulle kansa a bandaki, ya kuma ce gara ya kashe kansa da a kama shi a mikawa kasar Amurka.