Tukucin Amurka Bai Gurgunta Kokarinmu Na Sulhu Ba

Wata motar soja mai sulke dake sintiri tana tsaye karkashin bishiya a kauyen Hausari dake kusa da garin Maiduguri.

Shugaban kwamitin sulhu yace ba a taba tado da wannan batu a tattaunawar da suke yi da 'ya'yan kungiyar Boko Haram a wurare dabam-dabam ba.
Shugaban Kwamitin sulhunta rikice-rikicen arewacin Najeriya, kuma ministan ayyuka na musamman a gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan, Barrister Kabiru Tanimu Turaki, yace ayyukansu ba su fusknaci wata barazana ba a bayan da gwamnatin Amurka ta ce zata bayar da tukuicin daruruwan miliyoyin Naira ga wanda zai taimaka wajen kama shugaban kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnati Lidda'awati Wal jihad, ko Boko Haram, Imam Abubakar Shekau.

A cikin hirar da yayi da Muryar Amurka, Barrister Turaki yace wadanda suke taimakawa kwamitinsa domin ganin an samu sulhu a arewacin Najeriya, daga cikin jama'a har zuwa 'ya'yan kungiyar da suke tattaunawa da su, mutane ne da suke yin haka tsakani da Allah a saboda damuwar da suke da ita game da ganin an maido da zaman lafiya a wannan yanki.

Yace a duk tattaunawar da suke yi da 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram, babu wani bangaren da ya taba tayaer da wannan batu na tukuicin da gwamnatin Amurka ta ce zata bayar din.

Barrister Turaki yace 'yan kwamitinsa ba su ga yadda wannan abu zai kawo cikas ga ayyukansu ba, kuma da yardar Allah zasu cimma nasarar wannan yunkuri na samar da zaman lafiya mai dorewa a arewacin Najeriya.

Ga cikakken bayanin shugaban kwamitin...

Your browser doesn’t support HTML5

Tanimu Turaki Yace Tukuicin Amurka Na Kama Shekau Bai Zamo Musu Cikas Ba - 1:22