TUBALIN TSARO: Shirin Kasashen AES Na Kawar Da ‘Yan Ta’addan Yankin Sahel, Janairu 31, 2025

HAssan Maina Kaina

HAssan Maina Kaina

A shirin Tubali na wannan makon mun tattauna kan yadda Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso ke gab da kaddamar da ayyukan rundunar hadin gwiwa a karkashin inuwar kungiyar kawance ta AES, a ci gaba da jan damara a yakin da suke gwabzawa da ‘yan ta’addan yankin Sahel shekaru fiye da 10.

Shugabannin kasashen kungiyar AES - Nijar, Mali da Burkina Faso

Shugabannin kasashen kungiyar AES - Nijar, Mali da Burkina Faso

A baya wadanan kasashe sun kafa wata rundunar hadin gwiwa wato G5 Sahel da ta hada da kasashen Chadi da Mauritania, sai dai tsamin dangantakar da aka fuskanta a tsakanin kasashen na Sahel da Faransa ta haifar da durkushewar ayyukan rundunar.

Saurari cikakken shirin da Hassan Maina Kaina ya gabatar:

Your browser doesn’t support HTML5

TUBALIN TSARO: Shirin Kasashen AES Na Kawar Da ‘Yan Ta’addan Yankin Sahel, Disamba 31, 2024).MP3