Daya daga cikin mazaunan yanki da Mista Sunday Nwuka ya nuna rashin jin dadin lamarin inda ya ke cewa, "ni fa ba na son wannan. Ba dadinsa nake ji ba, a zauna a gida cewar me ya faru? Ba fa kowa ne ke jin dadin wannan ba, amma ya muka iya? Saboda idan har ka fita waje toh duk abin da faru da kai sai ka dauka hakan."
Sai dai wasu masu akidar Biafra irinsu Mista Remigus Okeafor na cewa, kasancewa a gida a kowace ranar Litinin shi ne abu mafi a'ala.
Ya ce, "kenan kana goyon bayan kada a ba mu Biafra? ina zaman gida saboda shugabanninmu ba sa mana adalci. Ba hanya, ba wutar lantarki, ba ruwa, bamu da komai muna shan wahala."
Shi ma Mazi Ikechukwu Okorie ya kara da cewa "ya kamata su sako mana mutuminmu. Tun da suna sakin 'yan Boko Haram suna cewa sun tuba, mu ma su sako mana mutuminmu Nnamdi Kanu saboda bai dace ya kasance a kulle ba,"
Yanzu yankin kudu maso gabashin Najeriya ya shiga wani mumunan yanayin ne, inda 'yan daba a daruruwansu kan zagaya unguwanni a kowace ranar Litinin suna tilasta wa jama'a su rufe shaguna tare da korar su cikin daka, lamarin da kan haddasa rashe-rashen rayuka sakamakon rikicin da kan barke tsakanin 'yan daban da jami'an tsaro, kamar yadda irin hakan ya faru a jihohin Anambra da Imo a 'yan kwanakin nan da suka wuce.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: