Tsokaci Kan Taron Kolin Kasashen Afrika

Shugabannin Kasashen Afrika

An bude taron kolin kasashen Afrika a kasar Habasha domin tattauna matsalolin da ke fuskantar nahiyar.

Da yawa daga cikin shugabannin kasashen Afrika yanzu haka na can Addis Ababa, babban birnin Habasha ko kuma Ethiopia, inda a yau Asabar aka bude taron kolin tarrayar kasashen Afrika, wato AU.

Babban batun da za a fi maida hankali a kai a wannan shi ne kare hakkin bil adama musamman da suka shafi mata.

Sannan za kuma a maida hankali kan rikicin siyasar kasar Burundi, inda kungiyar ta AU ke shirin aikawa da dakarun wanzar da zaman lafiya 5,000, domin kwantar da tarzomar da ta barke, wacce tuni ta lakume rayuka sama da 400.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari na daga cikin shugabannin da kae halartar wannan taro, kuma Halima Djimroa ta tuntubi mai ba shi shawar kan harkokin 'yan jarida, Malam Garba Shehu, wanda shi ma ke wajen taron domin jin karin bayani dangane da wannan taro.

Saurari cikakkiyar tattaunawar a nan:

Your browser doesn’t support HTML5

Tsokaci Kan Taron Kolin Kasashen Afrika- 6'00"