Tsohon shugaban gangamin yakin neman zaben shugaab Trump, Mr. Paul Manafort, ya saba yarjejeniyar da aka kulla tsakaninsa da masu bincike, bayan da ya yi karya.
Kwamitin bincike na musanman karkashin jagorancin Robert Mueller ne ya bayyana hakan a jiya Litinin.
Manafort, wanda mai yiwuwa ya fuskanci hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari, saboda aikata laifukan da suka shafi badakalar kudade, ya amince zai bai wa masu bincike hadin kai.
Idan ya ba da hadin kan, an amince za a yi watsi da wasu tuhume-tuhume, sannan a nema mai hukunci mara tsauri idan har ya fadi gaskiya a binciken.
Amma kwamitin na Mueller, da ke bincike kan ko gangamin yakin neman zaben Trump, ya hada kai da Rasha a zaben na 2016, ya bayyana cewa Manafort ya karya alkawarinsa da dokar kasa, saboda karerayin da ya yi.
Sai dai kwamitin na Mueller bai fito karara ya fadi karyar da Manafort ya yi ba.