Shugaban Namibia na yanzu Nangolo Mbumba ne ya sanar da mutuwar Nujoma a ranar Lahadi, wanda ya ce Nujoma ya rasu ne a daren ranar Asabar bayan da aka kwantar da shi a wani asibiti da ke babban birnin kasar, Windhoek.
Mbumba ya fada a cikin wata sanarwa da aka fitar cewa “An girgiza tubalin ginin Jamhuriyar Namibia.”
Ya ce “A cikin makonni uku da suka wuce, shugaban farko na Jamhuriyar Namibia kuma Uban Kasar Namibia yana kwance a asibiti domin jinya da duba lafiyar sa saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.”
Ya kara da cewa, “abin takaici, wannan karon, dan gwagwarmayar kasar mu ya kasa murmurewa daga rashin lafiyasa.”
Mbumba ya ce Nujoma “ya jagorancin al’ummar Namibia a lokaci mafi tsanani na gwagwarmayar ‘yantar da mu.”
Ana girmama Nujoma a kasarsa a matsayin uba mai kwarjini wanda ya jagoranci al’ummarsa zuwa ga dimokuradiyya da kwanciyar hankali bayan dogon mulkin mallaka da Jamus ta yi wa kasar da kuma yakin neman ‘yancin kai daga Afirka ta Kudu.
Ya kwashe kusan shekaru 30 yana gudun hijira a matsayin sa na jagoran fafutukar samun ‘yancin kai kafin ya koma zaben ‘yan majalisa a karshen shekarar 1989, zaben dimokaradiyya na farko a kasar.
‘Yan majalisa ne suka zaben shi shugaban kasa watanni bayan haka a shekarar 1990, yayin da Namibia ta samun ‘yanci kai.
Sai dai duk da hazakar sa da gina kasa a gida, Nujoma ya kan fito a kanun labarai na kasashen waje saboda zafafan kalamansa na kyamar kasashen yammacin duniya.