Tsohon shugaban ma'aikatan ya fito ne a karkashin inuwar jam'iyyar PDP kamar yadda aka yi zato idan an yi la'akari da jawabin gwamnan jihar na kwana kwanan nan.
A jawabin da ya gabatar Alhaji Umar Nasko yace yana da basirar yin aiki na cigaban jama'a duk da karancin shekarunsa.Idan har jam'iyyar PDP ta bashi dama za'asha mamaki, inji Nasko.
Taron ya samu halartar kusan kowane jami'in gwamnatin jihar. Kuma kusan duk 'yan majalisar dokokin jihar suka kasance a wurin taron. Shugaban majalisar Adamu Usman yace su a jihar Neja suna tafiya tare da gwamnati domin haka suna rokon Allah ya basu sa'a.
Sakataren gwamnatin jihar Neja Alhaji Idris Ndako shi ya wakilci gwamna Babangida Aliyu a taron. Idan ba'a manta ba gwamnan ya fada can baya cewa Allah ya nuna masa Nasko ne ya kamata ya gajeshi. A taron gwamnan yace ga amana nan ya baiwa jama'a.
Tsohon gwamnan Bayelsa da wasu kusoshin PDP sun halarci taron. Yanzu dai an samu 'yan takara takwas ke nan da suka fito a jam'iyyar PDP.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5