Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mukarraban Shugaba Jonathan Na Cigaba da Kare Tsayarda Shi Dan Takara


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan dan takarar PDP
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan dan takarar PDP

Mukarraban Jonathan da jam'iyyar PDP na cigaba da kare tsayarda shi dan takara daya tilo ba hamayya a zaben shekarar 2015

Amma abu mai daure kai shi ne karar da Farfasa Dupe Abiola tayi a babban kotun tarayya tana bukatar hukumar zabe kada ta bar kowa ma yayi takara a jam'yyar PDP din tunda jam'iyyar ta hanata takardar tsayawa takara.

Amma nan take jam'iyyar PDP tace da gangan ita Farfasa din ta ki zuwa karbar takardar takaran domin neman haddasa fitina.

Mai taimakawa shugaban ta fannin siyasa Farfasa Rufai Ahmed Alkali yace shugaban ya bada dama har ma ranar karshe kafin ya mika takardar takaran domin ba kowa taka rawa.

Farfasa Alkali yace babu wanda aka hanashi sayen takardar tsayawa takara. Ranar karshen sayen takardar 30 ga watan Oktoba ne amma bayan lokacin ya wuce sai da jam'iyyar ta sake bude ranar domin wanda bai sayi takardar ba ya je ya saya.

Sanata Haruna Goje da ya fice daga jam'iyyar PDP yace muddin aka yi zabe mai adalci jam'iyyarsu ta APC zata amshe madafin iko daga PDP ta aiwatar da canjin da zai amfani jama'ar kasar.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG