A jiya litinin ne, Tsohon shugaban kasar Masar Mohammaed Morsi, wanda shi ne shugaban kasar na farko da aka zaba bisa tsarin dimokradiyya aka kuma tsige shi, ya yanke jiki ya fadi kasa ya mutu a yayin wani zaman kotu.
WASHINGTON DC —
Jami’ai sun ce Morsi mai shekaru 67, ya yanke jiki ya fadi ne jiya Litini, bayan da ya kammala yin jawabi a gaban kotun yayin da ake sauraren shari’ar da ake masa ta zargin yin leken asiri.
Su ka ce Morsi ya yi jawabi na tsawon misalin minti biyar daga wani dan dakin gilashi da aka ajiye shi a lokacin sauraren karar, mintoci kadan kuma sai ya yanke jiki ya fadi kasa.
Tashar gidan talbijin din kasar ta ce, a lokacin da aka isa asibiti Morsi ya riga ya rasu.
A shekarar 2013, sojojin kasar suka hambarar da Morsi bayan zanga-zangar adawa da aka yi ta yi ma gwamnatinsa.