Likitoci sun ce da alamar hawan jini ne ya haifar da wannan halin da ya shiga, bayan da ya yi fama da wani mummunan bugun zuciya.
WASHINGTON, DC —
A watan Janairu ma an kai Peres, dan shekaru 93 da haihuwa asibiti saboda matsalar bugun zuciya.
Firaminista Benjamin Netanyahu ya buga wani sako a shafin Facebook mai cewa kasar baki daya na kaunar Peres kuma ta na masa kyakyawan fatan saurin waraka.
Peres ya bauta ma kasar Isira'ila a kusan dukkan manyan mukaman gwamnati, ciki har da zama Firaminista, Shugaban Kasa da kuma Ministan Harkokin Wajen Isra'ila. Da shi da Yasser Arafat da Yitzhak Rabin sun ci lambar yabo ta zaman lafiya ta Noble ta 1994, saboda taimakawa wajen cimma yarjajjeniyar zaman lafiya ta Oslo tsakanin Isira'ila da Falasdinawa.