A wani taro da cibiyar Chatam House da ke Landan ta shirya, Tsohon shugaban kuma daya daga cikin wadanda suke kan gaba wajen neman takarar shugaban kasa a karkashin babbar jam’iyyar adawa ta NDC a Ghana, John Dramani Mahama, ya gabatar da makala game da kudurorin Afrika.
Mahama ya fara da waiwayen yadda Afirka ta yi fama da illar mulkin mallaka, da kuma shekarun da aka yi fama da yawan juyin mulkin soja. Yana mai cewa a tsakanin shekarun 1980 zuwa da 1990, da taimakon wasu cibiyoyin tattalin arziki wasu kasashe suka fara farfadowa, musamman Ghana, bayan bankado 'yan kasar da Najeriya ta yi a 1983.
"Shekaru 30 da suka gabata, mun yi kokari wajen hada kan 'yan uwanmu kusan miliyan daya da aka kora daga Najeriya zuwa Ghana, ba tare da haifar da cikas ga tattalin arzikinmu ba. Manazarta sun ce korar kamar ramuwar gayya ce da Najeriya ta yi, bayan da aka kori wasu 'yan Afirka ciki har da 'yan Najeriya daga Ghana a karkashin dokar 'kasa-da-kasa ta 1969.
John Mahama ya zargi gwamnati mai mulki da ruguza tattalin arzikin Ghana da suka gada daga gare shi a shekarar 2017.
A bangaren shirin ci gaban karni mai dorewa, tsohon shugaban yace rashin aikin yi, da karancin hanyoyin bunkasa tattalin arziki, na ci gaba da fuskantar Afirka, lamarin da ke kara ta'azzara matasa kuma ana hasashen lamarin zai kara tabarbarewa nan da shekarar 2030 idan ba a magance ba, a cewar Mahama. Ya kara da cewa, babu shakka wannan barazana ce ga cimma burin ci gaban karni mai dorewa da kuma ajandar Afirka 2063.
Salahudeen Yunus Wakpenjo, yace abin jan hankali a jawabin shi ne yadda Mahama ya tabbatar wa masu zuba hannun jari daga kasashen waje cewa Ghana zata sake farfadowa bayan matsalolin tattalin arziki da kasar ke fuskanta.
Shi kuma a nasa ra'ayin Salihu Shu'aibu Sarauta, cewa ya yi bayani a kan yadda za a hada hannu da karfe wajen ci gaban Afirka, musamman ta bangaren kasuwanci shi ya fi jan hankalinsa a jawabin.
Chattam House dai cibiya ce mai zaman kanta da ke bincike kan manufofi da kudure-kuduren kasashen duniya, ta fannin siyasa, tattalin arziki, ilimi da sauransu.
Taron da aka yi ranar Juma'a na daga cikin abin da cibiyar Chatham House ke yi, don tattauna abubuwa na shugabancin kasashe musamman, wadanda suke tunkarar zabe domin gano manufofin ‘yan takara da kuma tantancesu.
Saurari rahoton Idris Abdullah Bako:
Your browser doesn’t support HTML5