Shi dai tsohon gwamnan jihar Taraba Danbaba Suntai wanda ya rasu a yau Laraba bayan fama da rashin lafiyar da yayi sakamakon hadarin jirgin sama, an haife shine a ranar 30 ga watan Yuni a shekarar 1961, kuma ya karanci ilimin hada magunguna wato pharmacist. An zabe shi a matsayin gwamna a inuwar jam’iyar PDP a watan Afrilun shekarar 2007, aka kuma rantsar da shi a ranar 29 ga watan mayun shekarar 2007.
Bayan nan kuma marigayi Danbaba Suntai ya sake tsayawa takarar tazarce inda aka sake zabensa a karo na biyu a ranar 26 ga watan afrilun shekarar 2011.
To sai dai bai kamala wannan wa’adi bane yayi hatsarin jirgin sama a Yola, lamarin da ya sake bude wani sabon babi a fagen siyasar jihar Taraba da ta kai nada mataimakinsa Garba Umar a matsayin mukaddashi ko da yake wasu kwamishinoninsa a lokacin wadanda akewa lakabi da yan kabal basu amince ba.
Haka nan tun bayan da aka dawo da shi daga kasar Amurka inda yake, Danbaba bai bayyana a bainar jama'a ba haka kuma bai ce uffan ba koda yake a wani bidiyo da ya fitar gwamnan ya godewa Allah da lafiyar da yake samu. Ya kuma shawarci 'yan Najeriya su koma ga Allah.
A cikin tausassar murya gwamnan ya ce yanzu ba zai iya komawa ofishinsa ba, amma yana rokon a taimaka masa domin a gaskiya baya cikin koshin lafiya ko kadan. Ya ce bashi da koshin lafiya da zai sa ya kama aiki ko domin wani ya goyi bayansa.
Emmanuel Bello tsohon kwamishinan yada labaransa shi ya tabbatar da rasuwan tsohon gwamnan.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5