Tuni dai wannan hukuncin kotun jihar Adamawan ya bude wani babi a yaki da cin hanci da rashawa da kuma sabawa ka’idojin aiki.
Shi dai tsohon gwamnan da yanzu haka ke gidan yari, Barista Bala James Ngillari, tare da magoya bayansa da suka hada da tsoffin kwamishinoni da hadimai da kuma sauran wadanda suka rike mukaman siyasa a zamaninsa tuni suka nufi kotun daukaka kara domin kalubalantar wannan hukunci da suke ganin akwai abin dubawa.
Da yake Karin haske tsohon kwamishinan yada labarai a zamanin Bala James Ngilarin, Abdullahi Adamu Prembe, ya ce suna da kwarin gwiwar samun nasara a kotun daukaka kara.
Wannan matsalar dai ta taso ne sakamakon kin bin ka’idar ayyukan hukumar kula da sayan kayakin gwamnati wato Bureau For Public Procurement BPP a takaice, lamarin da yasa aka kai ruwa rana har ta kai ga tunbuke babban daraktan hukumar
Tuni dai hukuncin kotun ya bude wani babi a yaki da cin hanci da rashawa da kuma sabawa ka’idojin aiki yayin da ya zuwa yanzu an zura ido aga yadda zata kaya a kotun daukaka ‘kara.
Domin karin bayani ga rahoton Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5