Tsohon Dan Wasan Ingila, Manchester United Bobby Charlton Ya Rasu

Allo dauke da hoton Bobby Charlton

Charlton wanda dan wasan tsakiya ne, ya shahara ne wajen kwarewa a fannin narka kwallo.

Fitaccen tsohon dan wasan Manchester United da Ingila Bobby Charlton ya rasu. Shekarunsa 86.

Charlton wanda ya shahara a fagen wasan kwallon kafa ya taba tsira daga wani hatsarin jirgin sama a shekarar 1958.

Wata sanarwa daga iyalan Charlton wacce United ta fitar, ta ce Charlton ya rasu ne zagaye da iyalansa.

Charlton wanda dan wasan tsakiya ne, ya shahara ne wajen kwarewa a fannin narka kwallo.

Shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a ragar har tsawon shekaru 40 sai daga baya Wayne Rooney ya doke shi.

Ya zura kwallo wa United 249 sannan ya zurawa kasarsa ta Ingila 49.

Ya bugawa Ingila wasa 106.