Tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya Manjo Janar Chris Alli Ya Rasu

CHRIS ALLI

Tsohon hafsan sojin ya rasu ne bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya da sanyin safiyar Lahadi a asibitin sojoji da ke Legas.

Bayan rasuwar tsohon babban hafsan soji, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya aika da sakon ta'aziyya a madadin sojojin Najeriya.

Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya-Gen. Onyema Nwachukwu ya fitar.

Kafin rasuwar marigayi tsohon COAS din ya yi hidima ga Sojojin Najeriya da ma kasa baki daya da daraja da kwazo a fannoni daban-daba.

Tsohon COAS din ya kasance ya yi aiki a wurare daban-daban inda ya nuna kwarewarsa wajen sauke nauyin daya rataya a wuyarsa.

Alli ya jajirce da kishinsa na aiki a fili yayin da ya kai matsayin Darakta, Hukumar Leken Asiri ta Soja (DMI), a cikin wasu manyan mukamai a cikin sojojin Najeriya.

Ya rike mukamin babban hafsan soji daga 1993 zuwa 1994 a karkashin mulkin Janar Sani Abacha sannan ya kasance gwamnan soja a jihar Filato daga watan Agusta 1985 zuwa 1986 a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida.

An haife shi a ranar 25 ga watan Disambar shekarar 1944, a Koton Karfe dake jihar Kogi, ya kuma yi ritaya daga aikin sojan Najeriya a matsayin Manjo Janar.