Tsoffin Takardun Kudade Za Su Ci Gaba Da Aiki ~ Babban Bankin Najeriya

Tsoffin Kudin Najeriya

Babban bankin Najeriya ya ce tsofaffin takardun kudi da ake shirin daina amfani da su a wata mai zuwa, yanzu za a ci gaba da aiki da su, hakan ya kawo karshen rashin tabbas na watanni bayan da yunkurin cire su a farkon wannan shekara ya haifar da karancin kudi.

WASHINGTON, D. C. - A watan Maris ne kotun kolin kasar ta umarci babban bankin Najeriya CBN ya tsawaita amfani da tsofaffin takardun kudaden 1,000 da 500 da kuma 200, wadanda cire su daga kasuwa ya zama batun zabe bayan da ya haifar da wahalhalu da tashin hankali.

Banban Bankin Najeriya CBN

Bankin ya kare matakin cire takardun kudaden, yana mai cewa zai yi wahala wajen yin jabun sabbin, sannan kuma tsarin zai taimaka wajen shawo kan matsalar tabarbarewar tattalin arzikin da ake rike da mafi yawan kudade a wajen bankuna.

A ranar Talata, CBN, wanda ya samu sabon gwamna tun watan Satumba, ya ce tsoffin takardun kudaden"za su ci gaba da kasancewa a matsayin kudi babu iyakar lokaci, har ma fiye da wa'adin farko na 30 ga watan Disambar 2023.”

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

A lokacin yakin neman zabe, shugaba Bola Tinubu ya nuna adawa da cire tsoffin takardun kudaden.

-Reuters