Domin magance wadannan matsalolin ne ya sa gwamnatin Najeriya a yanzu ta hada kai da sarakunan gargajiya da kuma yan Sakai da kuma shugabanin addini don gano bakin zaren magance wadannan matsaloli.
Mista Boss Gida Mustapha, dake zama sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya ya ce tuni wannan yunkuri Ya yi nisa.
Jihar Adamawa na daya daga cikin jihohin dake fama da matsalolin tsaro inda aka samu nasarar cafke wasu yan kungiyar gungun matasan nan dake addabar al'umma, da akewa lakabi da yan shila fiye da hamsin, yayin da wasu kuma suka mika wuya don neman ayi musu afuwa.
Ita kuwa a nata bangaren hukumar yaki da sha da fataucin muggan kwayoyi ta NDLEA tuni ta hada kai da wasu hukumomin tsaro don kawo karshen matsalar irin wadannan matasa, a cewar kwamandan hukumar a jihar Adamawa Mista Yakubu Kibo.
Domin Karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5