Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Osun Adegboyega Oyetola Ya Yi Nasara A Kotun Koli


Gwamna Adegboyega Oyetola
Gwamna Adegboyega Oyetola

A Najeriya Alkalan Kotun Koli 5 cikin 7 ne suka tabbatar da nasarar da gwamnan jihar Osun Adegboyega Oyetola na Jammiyyar APC yayi a zaben da ya gudana ranar 28 ga watan Satumbar shekarar 2018 da ta wuce.

Magoya bayan gwamnan a yau suna ta nuna farincikin su da bayyana ra'ayoyin su kan wannan nasarar da ta tsaida Adegboyega Oyetola a matsayin zababben gwamnan jihar Osun.

Dan takarar jamiyar PDP Sanata Ademola Adeleke ne ya daukaka kara zuwa kotun koli, amma lauyan gwamnan Oyetola a hirar sa da wakiliyar muryar Amurka, ya nuna tashi murnar, yace yanzu komai zai cigaba, don gwamnan zai natsu, ya koma kan aiki cikin kwanciyar hankali, don yin aikin da yakamata sosai a jihar Osun.

Ga rahoton Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG