Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Haji: An Gargadi Maniyyata


Gabannin fara jigilar alhazan Najeriya zuwa Saudiyya a Larabar nan, hukumar alhazan NAHCON ta gargadi alhazai su yi takatsantsan da duk abin da za su shiga da shi Saudiyya don kar wasu su yi musu sakiyar da ba ruwa.

Mukaddashin sakataren hukumar Ahmed Maigari ya ce la’akari da cusa kwaya da a ka yi wa Zainba Aliyu a lokacin Umrah, ya sa kiran ya zama wajibi don Saudiyya kan yanke hukuncin kisa ga irin wannan laifin.

Ita kuma jami’ar kula da abincin alhazai, Hajiya Ramatu Jafar Isa, ta ce akwai abinci mai tsafta da za a rabawa alhazan, don haka su guji cin abinci marar inganci daga Takari.

Tuni tawagar farko ta jami’an hukumar alhazai ta sauka a Madina don shirin tarbar alhazan karkashin jagorancin Muhammd Gire.

Shugaban hukumar alhazan Barista Abdullahi Muktar, ya ce masaukan alhazan na nan daf da harami a anguwar da ke zagaye da Haramin.

Jigilar alhazan dai za ta fara daga jihar Katsina da Kaduna da kuma Lagos.

Domin Karin bayani saurari cikakken rahotan Saleh Shehu Ashaka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG