Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da sabon shugaban hukumar Brigediya janar Mohammad Kaku Fadah ya cika kwanaki 100 da karban ragamar shugabancin hukumar inda ya ce an samu cigaba sosai ta fannoni da dama.
Cikin kwanaki dari da shugaban ya yi a jagorancin hukumar ta NYSC, ya zaga dukkan sansanonin ba da horo dake jihohi 36 a Najeriya ciki har da babban birnin tarayyar kasar Abuja don tabbatar da an samar da tsaro da inganta walwalar dalibai dake shirin yi wa kasa hidima ba tare da nuna gazawa ba, kana kaddamar da gidan talebijin da radiyo na hukumar da ma samar da cibiyar fasahar zamani na daga cikin nasarorin da hukumar NYSC ta cimma karkashin tsarin jagorancin sabon shugaban Brigediya janar Mohammad Kaku Fadah, wanda ya ce:
"a yanzu za’a mai da hankali ne kan gyara da sauye sauye a sansanonin bada horo la’akari da kusan shekaru 50 da kafuwar hukumar kuma dole ne ayi tafiya da zamani don samun cigaba."
Ko da yake dai shugaban ya ce rashin samar da isashen kuddade na aiwatar da wasu ayyukan su ke zama kalubale a garesu amma wani hanzari ba gudu ba, fatan su shi ne sa hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari ga kudurin samar da asusun tallafawa masu yi wa kasa hidima wanda tuni ya tsalake sa hannun majalisar wakilai da na dattawan kasar
Shugaban ya kuma zaburar da dalibai da su yi amfani da damar da hukumar ke badawa na koyar da ayyukan yi iri daban daban a sansanonin horar da su don dogaro da kawunansu ko bayan kammala aikin bautar kasa,
Hajiya Walida Sadiq Isa Shugabar sashin dake koyar da sanao’in hannu na hukumar NYSC wato SAED a takaice ta ce shekaru 10 da kafa sashin an samu tallafi daga bangarori da dama
A karshen dai shugaban hukumar ta NYSC ya yi kira da gwamnonin jihohi da shugabannin kananan hukumomi da su yi bakin kokarinsu wajen ba da taimako a gyare gyaren guraren ba da horo ga masu yi wa kasa hidima dake yankunansu don inganta manufar da aka kirkiri hukumar akai.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5