Yanzu dai ta tabbata cewa shugabanin jam’iyyar APC a jihohi na tare da gwamnoni wajen amfani da wakilai maimakon zaben kai tsaye na ‘yar tinke, don zaben fidda 'yan takara da ake shirin yi.
Wannan batu na ‘yar tinke ya janyo cece-kuce a tsakanin gwamnonin da ke da ra’ayin a yi amfani da wakilai da ake kira "delegates" da turanci wajen zaben dan takarar jam'iyya.
A daya bangaren kuma akwai wasu masu neman sauyi a jam’iyyar da suka hada da shugabanin jam’iyyar a tarayya da ke tare da ‘yan bangaren shugaba Buhari, da kuma shugaban jam’iyyar Adams Oshomole, wadanda ke rajin a yi amfani da tsarin 'yar tinke.
A wata hira da ya yi da wakilin Muryar Amurka, Sakataren tsare-tsaren jam'iyyar ya ce Ahmad Lawal ya ce "sun bi umurni kamar yadda uwar jam'iyya ta ba da umruni a yi na bin tsarin" kowa yake so.
Sai dai kuma wasu kusoshin jam’iyyar irinsu Alhaji Muhammad Iliyasu Gamawa, na ganin da walakin goro a miya, inda ya ce tsoro ne ya sa suke gani kamar idan ba su goyawa gwamnoni baya ba za a kore su.
Ya kara da cewa, wasu gwamnnonin na ikirarin cewa su gwamnonin talakawa ne, don haka gara a bambance tsakanin aya da tsakuwa.
Kamar Gamawa, shi ma Isa Ahmed Gwanjo, mai kula da gangamin yakin neman zaben Shugaba Buhari a jiha, ya ce ba zata sabu ba bindiga a ruwa. Yace makasudin zaben ‘yar tinke ana so a gano ko mutum yana da jama’a ne ko a’a.
Saurari karin bayanin wannan rahoto cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5