Yayinda ake cigaba da kirga kuri’u a wasu jihohi, bisa ga lissafin jiya Laraba Hillary Clinton nada kuri’u 2,017,563 fiye da Trump kuma zasu cigaba da karuwa saboda akwai kuri’un da har yanzu ba’a kidayasu ba a wasu jihohin da ta ci, musamman jihar California, jihar da ta fi kowace jiha girma da take yankin Pacific.
Ko menene ma ya faru, ko ta yaya kuri’unta suka karu, kuri’un da Clinton ta samu ba zasu canza sakamakon zaben da aka yi ranar 8 ga wannan watan Nuwamba ba. Zata zama ‘yar takara ta biyar a tarihin Amurka, kuma ta biyu cikin shekaru 16 da suka gabata da ta fi samun kuri’u amma kuma ta kasa cin zaben saboda Electoral College da aka kafa shekaru dari biyu yanzu. Kundun tsarin mulkin kasar ya dorawa Electoral College ikon zaban shugabannin kasar.
Zaben shugaban kasa a Amurka ya rataya ne akan kowace jiha da gundumar Kwalumbiya, wato Washington babban Birnin kasar. Duk wanda yaci kowace jiha zai samu kuri’un Electoral College na wannan jihar. Misali,idan jiha nada kuri’n Electoral Cllege 10 kawai komi girmanta, dan takarar da ya lashe zabe a jihar ya samu Electoral College goma ke nan. Babu kari babu ragi. Saboda haka kafin a ce mutum ya ci zaben shugaban kasa to dole sai ya samu kuri’un Electoral College 270 cikin jimillar 538. Jihar da ta fi girma ita ce take da kuri’un Ellectoral College ma fi yawa.
Trump ya ci jihohi da dama da ‘yar rata yayinda Clinton, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka wadda ta kyautata zaton zata zama shugabar kasa mace ta farko ta lashe kuri’un manyan jihohin California da New York. Nasara a wadannan jihohin ta sa ta fi Donald Trump kuri’u amma kuma zai karkare da kuri’un Electoral College 306 yayinda da ita kuma zata tashi da kuri’u 232 bayan da aka kammala kiyadayar duk kuri’un.
Trump hamshakin attajiri wanda biloniya ne yanzu yana fama da nada mukarrabansa da zasu yi aiki dashi a sabuwar gwamnatinsa. Ya taba yin tur da yin anfani da Electoral College wajen zaban shugabannin kasar sai dai kuma yace wata dabara ce dake da mahimmanci domin ta ba kananan jihohi damar yin tasiri a zaben shugaban kasa.
Ranar Talatan nan ya gayawa manema labaran jaridar New York Times cewa shi ya fi son yayi anfani da kuri’un jama’a kawai. Yace shi bai taba son Electoral College ba kafin yanzu saboda ta yin anfani da hanyar ce ya zama Shugaban Kasa Mai Jiran Gado
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5