Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Farko Kan Mulki Donald Trump Zai Janye Daga Yarjejeniyar TPP


Donald Trump
Donald Trump

Shugaban Amurka mai jiran gado ya ce ranar farko da zai fara aiki cikin abin da zai yi har da fidda sanarwar a hukumance cewa Amurka ta janye daga yarjejeniyar cinikayya da ake kira Trans-Pacific, ko TPP a takaice, abin da ke cikin jerin kudurorinsa akan sanya muradan Amurka kan gaba.

A wani sakon bidiyo da aka fidda jiya litinin, Trump ya kira yarjejeniyar cinikayyar a zaman wani bala’i ga Amurka.

Yace “maimakon haka, zai gudanar shawarwari akan kulla yarjejeniyar kasuwanci da za su maido da ayyukan yi da masana’antu Amurka.

A yakin neman zaben da yayi, Trump ya caccaki yarjejeniyar ta TPP, wanda suka hada da kasashe yankin Asiya da Pacific guda 12, da yarjejeniyar kasuwanci da kasar Canada da Mexico da ake kira NAFTA. Ya ce zai kulla wasu yarjejeniyoyin da zasu amfani Amurka.

Ministoci daga kasashen Trans-pacific sun rattaba hannu a watan Fabarairun shekarar nan, akan kudurin cewa zasu habaka cinikayya domin bunkasa tattalin arziki da samun al'umominsu, da samar da ayyukan yi.

XS
SM
MD
LG