Tsarin Ciyar Da Masu Ziyara A Watan Ramadana A Birnin Madina

Malam Hussaini Mohammad

A rahotannin mu da muke kawo muku na watan Ramadana, a yau DandalinVOA yayi nisan kiwo, domin kuwa muna birnin Madina dake kasar Saudia Arabia, inda zaku ji yadda tsarin ciyar da wadanda suka zo garin Madina ziyara a hanyarsu ta zuwa sauke faralin Umrah na watan Ramadana.

Malam Hussaini Mohammad, wanda ya fito daga jihar Kebbi a Najeriya, da ya shafe shekaru fiye da 20 a garin Madina, ya bayyana yadda tsarin ciyarwar bude baki yake a Saudiya, da ma yawan adadin kudaden da ake basu domin ciyarwar.

Hussaini Mohammad, ya ce tun da farko akwai wani bangaren da kasar Saudiya suke ware kudade, domin yi wa alumma hidima, mussamman ma lokacin watan Ramadana, ko da yake ya ce sai mutum na da alaka da gwamnati ne zai samu damar shiga rukunin wanda zasu samar da abincin shanruwa .

Ya ce akan basu Riyal dubu hamsin domin bada wannan abinci na ciyarwa, wato kwatankwacin naira miliyan biyar, yace a mafi yawan lokkuta, wasu daga cikinsu na fuskantar wasu matsaloli.

Ya ce daga cikin kalubalen da suke fuskanta shine na rashin kwanciyar hankali tare da tauye musu damamarki da kin amincewa da wasu wajen tabbatar da su a matsayin 'yan kasa.

Saurari cikakkiyar hirar su daga: Baraka Bashir.

Your browser doesn’t support HTML5

Buda baki a Madiana