Rikice-rikicen Boko haram ne ya tilastawa maihaifana dani muka yi hijira daga Jihar Yobe zuwa Kanon Dabo inda kasancewarmu baki a jihar rayuwa tayi mana tsananin abinda yasa na fara sana’ar sayar da waina da zuborado a gefen titi inji Aisha Bukar.
Matashiya Aisha Bukar ta ce bayan barowarsu daga Yobe rayuwa bata yi musu dadi ba domin ko na kaiwa baki ya kasance babban kalubale inda ta fara toya waina a gefen titi, ta kuma fara ne da kwanu biyu, har ta kai a yanzu suna toya kwanu goma na wainar shinkafa.
Ta kara da cewa suna tahowa ne tun daga garin Gezawa zuwa birnin Kano, inda su kan kwashe fiye da awa daya a cikin mota domin yin wannan sana’a a kullum, kuma tana farawa ne daga safiya har zuwa bayan la’asar.
Aisha ta ce tana da mataimaka sannan kanwarta na taimaka mata wajen wannan sana’a, ko da yake tana fusanta kalubalen rashin kallon kirki da wasu al’umma ke yi wa masu sana’ar abinci da fatan zasu kalli sana’ar abinci kamar kowace sana’a.
Your browser doesn’t support HTML5