Bikin na Kirsimeti da mabiya addinin Kirista ke yi a kowace shekara, yana zuwa ne da hada-hada da saye-sayen tufafi da sauran kayayyaki na cimaka.
To sai dai a bana wasu mabiya addinin Kirista zasu yi bikin ne dai-dai ruwa, dai-dai tsaki, saboda a cewar su, sun kaurace wa sayen sababbin tufafi sun koma sayen gwanjo, saboda tsadar rayuwa.
A hirar ta da Muryar Amurka, wata uwargida, Madam Eunice Godwin tace tsadar rayuwa ya sanya ta zuwa sayen kayan gwanjo. shima Mr Maren Zakariya yace, idan ba gwanjon suka saya ba, yaransu zasu yi Kirsimeti ne ba kaya, tunda kayan gwanjon sun fi na kanti sauki.
Malam Nafi'u Abdul'aziz, mai sai da kayan gwanjo a kasuwar Katako dake Jos, yace suma matsin rayuwar ya shafi harkokin kasuwancinsu, kuma suna tausaya wa kostomominsu.
Wani muhimmin sashe na bikin Kirsimeti shine yadda ake yanka kaji. Amma Kajin a bana farashinsu ya tsauwala, inda kaza daya ta kai naira dubu Ashirin, a cewar wadansu.
Shugaban kungiyar masu saida kaji a kasuwar Terminus dake Jos, Ibrahim Shehu yace, tsadar kajin ya sanya su yin taka tsan-tsan da kasuwar.
Duk da tsadar rayuwar, al’umma na fatar gwamnati zata sanya matakan samun sauki ga talaka, don shima yayi walwala.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5