Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bayyana takaicinsa a kan mummunan hatsarin da ya faru yayin bikin kalankuwar yara a birnin Ibadan wanda yayi sanadiyar asarar dimbin rayuka tare da jikkata wasu da dama.
Shugaban kasar ya mika sakon ta’aziyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Oyo, tare da iyalan dake alhinin rashin ‘ya’yansu.
“A wannan lokaci na alhini, shugaba tinubu na tare da iyalan da al’amarin ya shafa tare da gabatar da addu’o’in neman all.h ya gafaratawa wadanda suka rasu a hatsarin” a cewarsa.
Shugaba Tinubu ya kuma bada umarnin gaggawa ga hukumomin da suka dace domin su gudanar da cikakken binciki akan musabbabin afkuwar mummunan lamarin.
Dandalin Mu Tattauna