Tsabta Da Ado Ga 'Ya Mace Tamkar Ibada Ce - Inji 'Yan Mata

Kamar yadda muka ji daga bakin samari akan ado ko tasirin kwalliyar 'yan mata inda wasu daga cikin samarin suka yi masu kirari "mata adon gari", a wannan lokacin mun sami tattaunawa da 'yan mata ne inda suka bayyana mana irin nasu ra'ayin akan ado ko kwalliya.

Mata dai an san su da kwalliya a duk inda suke kuma masu iya magana sun ce tsabta cikon addini ce, dan haka kwalliya na daga cikin abubuwan da ke sa a gane mace mai tsabta.

kamar yadda wasu daga cikin 'yan matan suka bayyana, idan budurwa bata kwalliya ko kula da kanta, da wuya ta sami samari domin babu saurayin da zai so aga budurwar sa cikin dauda, haka ma kawayen ta baza su so tafiya da ita ba.

Yawancin lokuta 'yan mata kan yi kwalliya da lalle, kuma sukan canza nau'i nau'i daga lokaci zuwa lokaci harma wasu daga ciki sun lakanci yadda masu sana'ar ke yi dan haka suna yi dakan su.

Menene ra'ayin ku dangane da wannan hira? garzaya shafin mu na voahausafacebook domin tofa albarkacin baki.

Ga cikakkiyar hirar.