Da yake jawabi a wurin taron gangamin siyasa da yammacin shekaranjiya Laraba kafin zaben rabin wa’adi mako mai zuwa, Trump ya yi kokarin neman goyon bayan jama’a a kan shawarar da ya yanke ta soke dokar ‘yancin zama dan kasa ta haifuwa.
Yace a cikin lokaci kalilan idan suka shigo kasar mu, ‘ya’yan daruruwar bakin hauren da basu da iznin zaman kasar za su zama ‘yan kasa kai tsaye saboda wannan dokar marar ma'ana, kuma nan take sai su samu damar cin kowane amfani da duk wani ba-Amurke zai samu na biliyoyin dala a kowace shekara.
Trump ya kuma ce zai aika da sojoji dubu 15 a kan iyakar kasar da Mexico domin hana ayarin bakin haure daga tsakiyar nahiyar Amurka, wadanda suke niyar shigowa Amurka ba bisa ka’ida ba shiga kasar .
Trump ya bayyana bakin hauren a matsayin mutanen da ya kamata aji tsoronsu. Koda yake akasarin bakin hauren suna cewa suna so su shiga Amurka ne domin gujewa tashin hankalin kuma su samu rayuwa mai iganci da basu samu a kasarsu.